Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya (INEC) ta ce, duk da dage ranakun zabukan kasar, har yanzu ba a kai ga raba dukkan katunan zaben ba.
Hukumar ta INEC wadda ta bayyana hakan a wannan makon ta ce, ya zuwa yanzu katunan zabe na din-din-din miliyan 55.5 ta samu damar raba wa, wato kashi 80.61 cikin 100 na katuna miliyan 68.8 da aka buga a shekarar da ta gabata.
Ko da yake a baya wasu kwamishinonin hukumar a jihohin kasar, sun bayyana cewa, ba a kammala buga wasu daga cikin katunan zaben ba, wannan ya sa wasu mazauna birnin Abuja, babban birnin kasar ta Najeriya ke zargin hukumar zaben da nuna halin ba ruwa na wajen raba katunan zaben, yayin da wasu kuma ke zargin hukumar da kokarin danne hakkin jama'a na yin zabe.
Sai dai kakakin hukumar zaben Idowu ya ce, duk wanda sunansa ya fito a cikin kundin zabe zai samu katin nasa kafin ranar zabe.
A ranar Lahadin da ta gabata ne hukumar zaben Najeriya ta kara wa'adin karbar katunan zaben na din-din-din da makonni biyu wato har zuwa ranar 22 ga watan Maris, bayan da aka dage ranar zaben shugaban kasa zuwa 28 ga watan Maris, kana zaben gwamnoni aka gusar da shi zuwa ranar 11 ga watan Afrilu. (Ibrahim)