Karamin sakatare a MDD mai kula da ofishin siyasa, Jeffrey Feltman ya isa Nigeriya a ranar Litinin din nan don yin aikin yini biyu na goyon bayan gwamnati game da babban zaben dake tafe.
Ziyarar Mr. Feltman domin isar da sakon magatakardar MDD Ban Ki-moon ne game da muhimmancin aiwatar da babban zaben a ranar da hukumar zaben kasar INEC ta tsai da yanzu, in ji kakakin majalissar Farhan Haq.
Kakakin ya yi bayanin cewa, a lokacin ziyarar, Jeffrey Feltman zai ba da kwarin gwiwwa ga dukkan hukumomin kasar da su hada kai tare da hukumar zaben domin tabbatar da 'yan Nigeriya sun samu damar sauken hakkinsu a matsayin 'yan kasa a wannan ranar da aka tsai da.
An dai tsai da gudanar da zaben shugaban kasa da majalissar dokoki a ranar 28 ga watan nan na Maris, sannan kuma na gwamnoni da majalissar wakilai a ranar 11 ga watan Afrilu. Tun da farko, an shirya yin zabukan ne a ranakun 14 da 28 ga watan Fabarairun da ya gabata, amma aka dage bisa dalilan tsaron, musamman kungiyar 'yan ta'addan nan na Boko Haram. (Fatimah)