Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC Farfesa Attahiru Jega, ya yi watsi da jita-jitar dake yaduwa, cewa wai zai ajiye aikinsa gabanin manyan zabukan kasar dake tafe.
Farfesa Jega wanda ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a birnin tarayyar Najeriya Abuja, ya kara da cewa, batun ya yi murabus kafin zaben tamkar yiwa kasar makarkashiya ne.
Kaza lika shugaban hukumar ta INEC ya karyata rade-radin da ake yi cewa, yana fuskantar matsin lamba game da batun ajiye aikin nasa.
Game da shirye-shiryen da hukumar zaben ke yi kuwa, Jega ya ce, INEC tana da shirin baiwa ragowar mutane 700,000 wadanda har yanzu ba su karbi katunan zabensu na din din din ba katunan nasu nan da ranar Asabar.
Ya ce, ya zuwa yanzu an raba kaso 80.61 na katunan ga 'yan Najeriya, kuma ko shakka babu za a yi amfani da na'urar tantance masu kada kudi'u kamar yadda aka tsara, duk kuwa da kalubalen da hakan ke fuskanta daga wasu bangarori.
Za dai a kara kuri'un zaben shugaban kasa da 'yan majalissun tarayyar Najeriya ne a ranar 28 ga watan nan na Maris, yayin da kuma zaben gwamnoni da 'yan majalissun jihohi zai biyo baya a ranar 11 ga watan Afirilu. (Saminu)