Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya (INEC) ta sanar da kara lokacin karbar katin zabe na din-din-din ya zuwa makonni biyu gabanin zabukan kasar da ke tafe a kasar.
Wata sanarwa da kakakin hukumar Kayode Idowu ya rabawa manema labarai ta nuna cewa, za a ci gaba da raba katunan a dukkan fadin kasar har zuwa ranar 22 ga watan Maris, wato kwanaki shida kafin ranar da za a yi zaben shugaban kasa.
Hukumar ta ce, ta dauki wannan mataki a karo na biyu ne don ba da dama ta karshe ga wadanda suka cancanci kada kuri'a 'yancin zabar 'yan takarar da suke bukata a zabukan da ke tafe.
A watan da ya gabata ne hukumar ta INEC ta kara wa'adin karbar katunan zaben sakamakon dage zabukan kasar daga ranar 14 ga watan Fabrairu zuwa 28 ga watan Maris, yayin da za a gudanar da zaben gwamnoni a ranar 11 ga watan Afrilu. (Ibrahim)