Kwararrun tawagar MDD dake kasar Cote d'Ivoire (ONUCI) na dukufa wajen warware rikicin dake kamari tsakanin manoma da makiyayya a arewacin kasar, a wani labarin da Xinhua ya samu daga wata majiyar MDD a ranar Lahadi.
A cewar wani ofisan bangaren da ke kula da harkokin fararen hula na ONUCI mista Peyogori Ouattara, kwararru da hukumomin wuraren na yankunan dake arewacin kasar sun hada kokarinsu tare domin kai ga cimma wata hanyar sulhu tsakanin manoman da makiyayan.
Mista Ouattara ya yi amfani da misali na yankin Bako dake arewacin kasar, inda manoma da makiyayya suka cimma yarjejeniyar kawo karshen duk wani rikici da tashin hankali tsakaninsu. (Maman Ada)