in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya dagewa Kwadibuwa takunkumin fitar da lu'u lu'u
2014-04-30 10:55:54 cri

Sakamakon abin da da kwamitin tsaron MDD ya bayyana da kyautatuwar yanayin tsaro a kwadibuwa, yanzu haka kwamitin ya dage takunkumin da ya kakabawa kasar game da batun cinikayyar lu'u lu'unta. Tare da bukatar gwamnatin kasar ta sanar da cikakken shirinta, na bunkasa sashen ma'adanin na lu'u lu'u.

Har ila yau kwamitin ya sabunta wa'adin takunkumin cinikayyar makaman kasar masu hadari kwarai. An dai tsawaita wa'adin takunkumin irin wadannan makamai ne da shekara guda. Yayin da a hannu guda takunkumin a yanzu ya kebe makamai marasa hadari, da kayayyakin aikin soji na kyautata tsaro, wadanda kasar ke da ikon mallaka, ba tare da neman izinin kwamitin lura da takunkumin ba.

An dai kakabawa Kwadibuwa takunkumin hana mallakar makamai ne a watan Nuwambar shekarar 2004, yayin da kuma takunkumin cinikayyar lu'u lu'u ya fara aiki cikin watan Disambar shekarar 2005. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China