in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta kaddamar da aikin gyaran dokar kafa dokokin kasar
2015-03-09 15:23:23 cri

A jiya Lahadi 8 ga wata ne wakilan jama'ar kasar Sin kimanin 3000, suka saurari bayani kan daftarin gyararren shirin dokar da ta shafi kafa dokokin kasar, matakin da ya kasance karo na farko da wakilan jama'ar na wannan karo na 12, suka tattauna kan shirin doka a yayin babban taron NPC, tun bayan da suka fara gudanar da ayyukansu a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Idan har an zartas da wannan shirin doka, hakan zai kasance doka ta farko da aka aiwatar a wannan shekarar da muke ciki.

"A halin yanzu, a kan daidaita yawan harajin da ake karba, ba tare da yin la'akari sosai ba. Idan an tsai da kuduri kan wannan batu bisa aniyar wata hukuma ta gudanar da harkokin kasa kawai a maimakon wata doka, hakan na iya haddasa mummunan sakamako."

A farkon wannan shekarar da muke ciki, ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta kara yawan harajin man fetur har sau uku a cikin watanni biyu kacal, matakin da ya yi matukar janyo hankalin al'umma. Hakan ya kuma kara kwarin gwiwar wakiliyar jama'ar kasar Sin Madam Zhao Dongling, wajen yin kira kan batun karbar haraji bisa doka. Yau shekaru biyu ke nan tun bayan da Madam Zhao da sauran wakilan jama'a 31 suka gabatar da shirinsu, inda suka yi kira ga majalisar wakilan jama'ar kasar da ta samar da ikon kafa dokar haraji. Yanzu haka kuma an kai ga bada amsa kan wannan shiri, a cikin daftarin gyararren shirin doka kan kafa dokokin kasar.

Da yammacin ranar 8 ga wata, Li Jianguo, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jam'ar kasar Sin ya yi wa wakilan jama'a bayani, game da wannan daftarin gyararren shiri. Yayin da ya tabo batu game da karbar haraji bisa doka, wakilan jama'a sun yi tafi domin nuna maraba da hakan.

"Daftarin gyararren shirin dokar ya yi tanadi game da batun karbar wani irin haraji, da dakatar da wani, kana da gudanar da ayyuka masu alaka da hakan, musamman wadanda ba a iya gudanar da su ta sauran hanyoyiba , sai dai bisa doka kawai."

Yanzu kasar Sin tana da nau'o'in haraji 18, ban da harajin kudin shiga na masana'antu, da harajin kudin shiga na jama'a, kana da harajin motoci da jiragen ruwa, wadanda ake karba bisa dokar da majalisar wakilan jama'ar Sin ta kafa, sauran nau'o'in haraji 15 an kaddamar da su ne bisa amincewar majalisar gudanarwa ta kasar. A ganin Madam Zhao Dongling, hukumomin gudanarwa suna karbar haraji, bayan sun kafa doka kan harajin da kansu, lallai hakan bai yi daidai da adalci ba.

Idan mun waiwayi tarihin gyaran shirin doka kan kafa dokokin kasar, muna iya gano cewa, akwai dimbin bukatu kamar "karbar haraji bisa doka" wanda zai dace da aikin karfafa yin gyare-gyare a kasar Sin.

Dokar kafa dokoki da ake amfani da ita, an kafa ta ne a shekarar 2000. A wannan karo an sake gudanar da gyare-gyare kan wannan doka ne, domin daidaita dangantaka tsakanin batun kafa doka da aikin gyare-gyare, a kokarin samar da moriya ga aikin kafa doka ta jagoranci, ta yadda za a iya tabbatar da yin babbar kwaskwarima bisa doka.

Sai dai yayin da ake aiwatar da wannan aiki, akwai wata matsalar da take zama barazana ga aikin kwaskwarimar, musamman idan an yi la'akari da moriyar hukumomin gudanarwa yayin da ake kafa doka. Ma Huaide, mataimakin shugaban jami'ar koyon ilmin dokoki da shari'a ta kasar Sin ya nuna cewa,

"Yanzu a cikin dokoki fiye da 240 da majalisar dokokin kasar Sin ta fitar, dokokin da yawansu ya zarce kashi 90 cikin kashi dari, hukumomin gwamnatin kasar Sin ne suka tsara su, sannan nan majalisar ta tattaunawa ta kuma zartas da su, hakan ya sa a kan samu muradun hukumomin a cikin wasu dokoki."

An gyara shirin doka kan kafa dokoki ne domin jaddada muhimmin matsayin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a cikin aikin kafa doka, za a tsara jerin shirye-shirye, don gudanar da aikin kafa doka yadda ya kamata. Li Jianguo ya ce,

"Kwamitin musamman, da hukumomin zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, za su iya sa hannu kan aikin tsara daftarin shirin dokoki. Game da wasu daftarin shirin doka da za su shafi fannoni da dama kuwa, kwamitin musamman, ko hukumomin zaunannen kwamitin majalisar za su iya ba da jagoranci wajen tsara su."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China