in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dole ne a kara kokarin kyautata zaman rayuwar jama'a in ji firaministan kasar Sin
2015-03-06 15:45:21 cri

A yau Jumma'a ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada bukatar kara kwazo wajen aikin raya zaman al'ummar Sin a zamanance. Yana mai cewa dole ne a dogara da karfi, da basirar daukacin jama'ar kasar, a fagen neman samun ci gaba cikin sauri kuma yadda ya kamata, ta yadda za a cimma burin kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar.

Mr. Li Keqiang ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa tare da kungiyar wakilan lardin Shandong, game da rahoton aikin gwamnati.

Ya ce a shekarar 2014, sakamakon raya aikin kirkire- kirkire, da kokarin kafa sabbin kamfannoni masu inganci, an samu karuwar yawan sabbin guraban ayyukan yi, duk da kasancewar raguwar saurin karuwar ci gaban tattalin arziki a nan kasar. Hakan ya nuna cewa, tattalin arzikin Sin na da makoma mai kyau.

Haka zalika, firaminista Li Keqiang ya ce, a halin da ake ciki a fannin tattalin arziki, za a kara samun kyakkyawan sakamako a nan gaba, idan aka ci gaba da raya aikin cikin sauri. Amma hakan ba zai samu ba har sai an raya tattalin arziki mai inganci. Ta haka za a kai ga cimma burin raya zamantakewar al'ummar Sin a zamanance, tare da kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar ta Sin yadda ya kamata.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China