in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fadada zuba jari ba ya nufin sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin kasar Sin inji Xu Shaoshi
2015-03-06 16:33:43 cri

Yayin taron manema labaru game da taro na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12 da aka gudanar a jiya Alhamis 5 ga wata, shugaban kwamitin raya kasa, da yin kwaskwarima na kasar Sin Xu Shaoshi ya bayyana cewa, za a fuskanci matsin lamba a fannin tattalin arzikin Sin a shekarar 2015, sai dai duk da haka akwai kyakkyawar makoma, da imanin samun bunkasuwa a wannan fanni.

Ya ce, za a fadada zuba jari a shekarar 2015, don bunkasa tattalin arzikin Sin, amma wannan ba ya nufin sa kaimi kwarai da gaske, ga bunkasa tattalin arzikin kasar.

A shekarar 2014, saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin ya karu da kashi 7.4 cikin dari, wanda shi ne mafi karanci a tarihi bayan shiga karni na 21, don haka bangarori daban daban sun nuna damuwa ga yiwuwar raguwar tattalin arzikin kasar Sin. Game da hakan, Xu Shaoshi ya bayyana cewa, an fi fuskantar mawuyacin hali a shekarar 2014, yayin da ake bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma a kasar Sin, amma sakamako ya yi kyau sama da abin da aka zata.

Ya ce Sin ta bunkasa tattalin arzikin ta yadda ya kamata, ta kuma kiyaye farashin kaya, da tabbatar da samar da aikin yi a shekarar. Xu ya bayyana cewa,

"A shekarar 2014, an samu nasarori kan raya tattalin arziki, da zamantakewar al'ummar kasar Sin. Na farko, an bunkasa tattalin arziki yadda ya kamata, wanda alkalumansa suka karu da kashi 7.4 cikin dari bisa na shekarar 2013. Na biyu, an tabbatar da farashin kaya a kasar, inda yawan ma'aunin farashin kayayyakin da jama'a ke amfani da su wato CPI a shekarar ya karu da kashi 2 cikin dari, adadin da ya yi kasa sosai. Na uku kuma, an tabbatar da samar da aikin yi a kasar. A wannan fanni yawan mutane mazauna birane da kauyuka da suka samu aikin yi a shekarar 2014 ya kai miliyan 13 da dubu 220, sama da hasashen da aka yi a wannan fanni."

Game da halin tattalin arzikin kasar Sin daga manyan fannoni a shekarar 2015 kuwa, Xu Shaoshi ya bayyana cewa, kasancewar ana fuskantar matsaloli a cikin gida da waje, akwai matsin lamba wajen magance raguwar tattalin arzikin kasar Sin. Duk da hakan a cewarsa akwai kyakkyawar makoma, da imanin samun bunkasuwa a wannan fanni.

Ya ce an riga an gabatar da alkaluma game da tattalin arzikin Sin na watan Janairu da na Febrairun bana, koda yake yawan cinikin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, da na shigar da kayayyaki cikin kasar Sin, da kuma CPI da PPI na kasar Sin a watan Janairu ya ragu, a hannu guda kuma adadin ya karu kadan a watan Fabrairu. A ganin Xu Shaoshi, wannan ya bayyana cewa, ana bin tafarkin da ake kai, tare da karfin gwiwar kasuwanni. Xu ya jaddada cewa, ana shiga sabon tsarin yau da kullum na tattalin arzikin Sin, kuma yana da kyakkyawar makoma. Ya ce,

"Ko da yake saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin ya ragu, amma ba a samu raguwar tattalin arzikin akai-akai ba. Ko da yake yana da wuya a rage yawan kayayyakin da suka wuce kima, amma sabbin sha'anoni suna samun bunkasuwa. Ko da yake akwai hadari yayin da ake raya tattalin arziki, amma muna iya yin amfani da matakan daidaitawa, don inganta tattalin arziki, muna da imanin cimma wannan buri."

A cikin rahoton ayyukan gwamnatin kasar Sin da aka gabatar a ranar 5 ga wata, an ce, gwamnatin kasar Sin ta tsara burin karuwar yawan GDP na kasar na shekarar 2015 da kashi 7 cikin dari. Don cimma wannan buri, kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima, ya bayyana cewa, kamata ya yi a maida hankali ga sabbin fannoni dake sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki, da kuma kafa sabbin ziri, kamar zirin tattalin arziki na siliki, da hanyar Siliki ta ruwa ta karini na 21, da zirin tattalin arziki na Beijing, da Tianjin, da lardin Hebei, da zirin tattalin arziki na kogin Yangtse da dai sauransu.

Xu ya bayyana cewa, ya kamata kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya yi kwaskwarima daga fannoni hudu. Ya ce,

"Wadannan fannoni hudu su ne kwaskwarima a tsarin neman iznin yin wani abu, da tsarin samun amincewa, da tsarin hada-hadar kudi da kuma tsarin farashin kaya. A ganina, ba za a zurfafa yin kwaskwarima ba, har sai an yi kwaskwarima cikin kuzari tun da farko."

Ban da yin kwaskwarima, kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya dauki matakai da dama, wajen kara zuba jari a fannonin sadarwa, da wutar lantarki, da iskar gas. Sauran su ne yanar gizo, da makamashi mai tsabta, da hanyoyin jiragen kasa, da manyan ayyukan samar da wutar lantarki ta karfin ruwa da dai sauransu. Duk kuwa da cewa matakan sun jawo damuwa daga bangarori daban daban. Wadanda ke janyo tambayar ko an fara sa kaimi kwarai da gaske ga sabon zagaye ga bunkasar tattalin arzikin kasar Sin ko kuwa a'a? Game da wannan, Xu ya bayyana cewa,

"Sin babbar kasa ce wadda ke kokarin raya masana'antu, da zamanintar da yankunanta, don haka muna bukatar da kara zuba jari a wasu muhimman fannoni. Don haka ba a bukatar sa kaimi kwarai ga bunkasuwar tattalin arzikin kasa. Matsalarmu ita ce zuba jari ga fannonin da ake bukata." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China