in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin kasar Sin na bunkasa yadda ya kamata, in ji Li Keqiang
2015-03-05 10:57:55 cri

A yau Alhamis, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da rahoton aikin gwamnatin kasar Sin, a gun taro na 3 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12, inda ya ce a bara tattalin arzikin kasar Sin ya samu bunkasuwa yadda ya kamata.

Li Keqiang ya ce, saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ya dace da halin da ake ciki yanzu. Kuma yawan GNP da aka samu ya kai kudin Sin RMB biliyan 63600, wanda ya karu da kashi 7.4 cikin dari, idan aka kwatanta shi da na shekarar da ta gabace ta. Ya ce wannan adadi ya zama a matsayin koli a duniya.

A wani bangaren na daban kuma, Mr. Li ya ce yawan guraban ayyukan yi ya karu yadda ya kamata, kana yawan karuwar sabbin guraban ayyukan yi da aka samar a birane da garuruwa ya kai miliyan 13 da dubu 220, wanda ya karu, idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabace ta. Haka zalika kuma, farashin kayayyaki ya karu yadda ya kamata, inda ya daga da kashi 2 cikin dari.

Ban da haka kuma, a cewar sa an kara samun bunkasuwa mai dorewa da kuma daidaito. Tsarin tattalin arziki na ci gaba da samun kyautatuwa, kuma yawan hatsin da aka samar ya kai kilogiram biliyan 605, yayin da yawan kudin da aka kashe wajen sayen kayayyaki ya karu, adadin da ya dauki kashi 51.2 cikin dari, daga cikin daukacin yawan karuwar tattalin arzikin kasar. Kaza lika yawan karuwar kudin da aka samu daga sana'ar ba da hidima ya karu daga 46.9 zuwa 48.2 cikin dari, inda ake ta samun sabbin sana'o'i da sabbin ire-iren kasuwanci masu dama.

Ban da haka kuma, zaman rayuwar jama'a na samun sabuwar kyautatuwa, kuma yawan kudin da kowane mutum ke samu ya karu da kashi 8 cikin dari, wanda ya nuna saurin bunkasuwar tattalin arziki. Cikin wannan adadi akwai mutanen dake zaune a kauyuka da ya kai kasha 9.2 cikin dari, wanda ya fi na birane saurin samun ci gaba. Haka kuma, yawan matalauta dake kauyuka ya ragu da miliyan 12 da dubu 320.

Sai kuma batun karancin ruwan sha da manoma miliyan 66 suke fuskanta, wanda a yanzu aka samu sassauci a kan sa. Inda a hannu guda kuma yawan masu yawon shakatawa zuwa kasashen waje ya kai mutum miliyan 100.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China