Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya sake jaddada kira ga daukacin masu ruwa da tsaki, da su zage-damtse wajen tabbatar da nasarar shirin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu.
Hakan dai na zuwa ne bayan da bangarorin kasar biyu suka amince da wata sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin su.
Cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Mr. Ban ya jaddada cewa, babu wata nasara da za a cimma a Sudan ta Kudun, muddin shuwagabannin bangarorin kasar biyu suka ki amincewa, su sanya bukatun al'ummun kasar gaban nasu muradun.
Mr. Ban ya kuma bukace su, da su shirya tinkarar zagaye na biyu na ganawar da za su gudanar, da niyar gaggauta kawo karshen rikicin kasar baki daya.
Kaza lika babban magatakardar MDDr ya jinjinawa kungiyar shuwagabannin kasashen gabashin Afirka ta IGAD, bisa shiga tsakani da ta yi a rikicin kasar ta Sudan ta Kudu.
Kungiyar ta IGAD ce dai ta jagoranci shirin shiga tsakani, wanda ya kai ga cimma matsaya guda tsakanin shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir, da shugaban 'yan adawa, kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar, yayin zaman sulhun da ya gudana a ranar Litinin, a birnin Addis Ababan kasar Habasha. Yarjejeniyar da aka cimma ta kuma tanaji sake tattaunawa, a wani mataki na kammala shirin wanzar da zaman lafiya, daga nan zuwa 5 ga watan Maris mai zuwa. (Saminu)