in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta zargi 'yan tawaye da saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta
2015-02-09 10:21:37 cri

Sojojin kasar Sudan ta Kudu sun zargi sojojin 'yan tawaye karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar da saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta, inda suka yi luguden wuta a kan wuraren dake karkashin ikon sojin sudan ta Kudun.

Kakakin sojin na Sudan ta Kudun Philip Aguer ya shaida wa Xinhua cewa, sojojin Machar ba su bi yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu a kai ba ta tsagaita bude wuta duk da ya tabbatar da cewar, sojojin na Sudan ta Kudu za su dage na ganin sun bi wannan yarjejeniyar da suka amince sai dai har in an tilasta masu kare kansu su ne kawai za su mai da martani ga 'yan tawayen.

Shugaban kasar na Sudan ta Kudu, Salva Kiir Mayardit da shugaban 'yan tawayen Riek Machar a ranar 2 ga watan nan suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, rabon ikon kasar, da kuma kafa gwamnatin rikon kwarya kafin a cimma wata matsaya ta kawo karshen tashin hankalin dake wakana a tsakaninsu nan da 5 ga watan Maris.

Mai shiga tsakani daga kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afrika IGAD, Seyoun Mesfin tun da farko ya sanar da cewa, ana sa ran masu gaba da juna su biyun daga kasar Sudan ta Kudu za su rattaba hannu a kan yarjejeniya ta kashe a ranar 20 ga watan nan na Fabrairu. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China