Wani kazamin artabo ya abku tsakanin wani gungun mayakan kungiyar Boko Haram dake Najeriya da sojojin kasar Nijar dake sintiri a ranar Talata a jihar Diffa dake iyaka da tarayyar Najeriya, musanyar wutar da ya yi sanadiyyar mutuwar mayakan Boko Haram biyu, in ji hukumonin kasar Nijar a ranar Laraba a birnin Niamey.
Magajin garin jihar Diffa Younoussa Samna, ya ba da labarin ga wata kafar ketare ba tare da ba da wani karin haske ba.
Kungiyar Boko Haram, dake hadabar arewacin Najeriya tun a shekarar 2009 ta hanyar kai hare-haren ta'addanci, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar miliyoyin jama'a da tilastawa mutane kaura zuwa kasashe makwabta, musammun ma kasar Nijar.
Aikin aika aika da kungiyar ta yi na baya bayan nan shi ne sace dalibai mata 276 na makarantar sakanden Chibok a arewa maso gabashin kasar Najeriya a ranar 14 ga watan Afrilun da ya gabata.
Tun wannan lokaci ne, gwamnatocin kasashen dake makwabtaka da Najeriya, musammun ma Nijar suka tsaurara matakan tsaro a kan iyakokinsu.
Kasashen Nijar da Najeriya, suna makwabtaka da juna, kuma suna raba iyaka guda bisa tsawon fiye da kilomita 1500, yawancin al'umominsu musulmi, kuma suna magana da harsunan Hausa, Fulatanci da Kanuri. (Maman Ada)