in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta bukaci taimakon kasa da kasa dalilin karuwar 'yan gudun hijira sakamakon harin Boko Haram
2014-12-15 10:44:12 cri

Gwamnatin kasar Nijar ta yi wani kiran neman taimakon kasa da kasa domin daukar nauyin dubayan 'yan gudun hijirar Najeriya, dake kasarta, wadanda ke gudu saboda harin kungiyar Boka Haram, domin kaucewa masifar jin kai da za ta faru, a cewar hukumomin kasar Nijar.

A gaban hare hare da kashe kashen mutane da kungiyar Boko Haram ke aikatawa a garuruwansu, musammun ma kwace garin Damasak a baya bayan nan, dake kusa da iyaka da kasar Nijar, a kalla kusan mutane 115,000 suka samu mafaka a jihar Diffa, dake gabashin Nijar da kuma ke iyaka da Najeriya. Matsalar a yankin Gagamari na jihar Diffa, da ya karbi a cikin sati, kusan 'yan gudun hijira 17,000, lamarin da ya ninka sau biyar bisa ga yawan al'ummar wurin, lamarin da ya kasance wani matsin lambar na zuwan 'yan gudun hijirar kan zaman rayuwar al'umma, da ma tattalin arzikin wannan yanki na kasar Nijar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China