Ministan tsaron kasar Nijar Karidjo Mahamadou, da ke ziyarar aiki a jihar Diffa, da ta yi fama da munanan hare haren kungiyar Boko Haram ta Najeriya a 'yan kwanaki uku na bayan bayan nan, ya yi kira a ranar Lahadi ga 'yan majalisar dokokin Nijar da su ba da amincewarsu cikin gaggawa ga rundunar sojojin Nijar da su shiga Najeriya domin ba da goyon baya domin fatattakar mayakan kungiyar Boko Haram.
Yankunan Bosso da Diffa dake gabashin kasar dake iyaka da Najeriya sun fuskanci hare haren Boko Haram guda uku tsakanin ranar Jumma'a da Lahadi tun daga sansanoninsu dake Najeriya, hare haren da suka janyo mutuwar mutane shida da suka hada da sojojin Nijar guda hudu, tare da jikkata sojoji da fararen hula kusan talatin. (Maman Ada)