A daren jiya ne wata tawagar masu fasaha mai suna "murnar bikin bazara na shekarar 2015 a kasashen waje" da ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ta tura ta yi kasaitaccen bikin nune-nune a Zimbabwe, domin nuna gaisuwar bikin bazara ga Sinawa dake kasar.
Wannan tawaga mai kunshe da masu fasaha 32, galibinsu sun fito ne daga birnin Tianjin, wadanda suka gabatar da wake-wake da raye-raye da fasahar kundunbala da kuma wasan Kongfu da dai sauransu. Ban da haka kuma, magada kayayyakin tarihin al'adu 4 daga lardin Liaoning sun nuna fasahar yanka takarda, da kayan sassaka da aka yi da gari, da zane-zanen da aka yi da yatsu, da kuma sauran wasannin fasaha na musamman na kasar Sin. Wadannan nune-nunen da suka yi sun samu yabo sosai daga 'yan kallo.
Rahotanni na cewa, an shafe shekaru da yawa ana nune-nunen murnar bikin bazara a kasashen waje, kuma ya zama babban aikin al'adu da ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ta yi a kasashen waje. Daga karshen watan Janairu zuwa tsakiyar watan Maris na wannan shekara, tawagogin fasaha 6 na kasar Sin za su kai ziyara a kasashe 9 na Afrika domin gabatar nune-nunen taya murnar bikin bazara.(Lami)