in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya nada ministan shari'a a matsayin mataimakinsa
2014-12-11 10:09:21 cri

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya bayyana sunan ministan shari'a na kasar Emmerson Mnangagwa, mai ra'ayin rikau a matsayin mataimakin shugaban kasar, kana kuma mataimakin shugaban jam'iyyar ZANU PF mai mulkin kasar.

Shi dai sabon mataimakin shugaban kasar ya maye gurbin madam Joice Mujuru, wacce Mugabe ya sallama bayan an yi mata zargin aikata kisan kai.

Mr. Emerson, ana yi masa kallon yana shugabantar wani bangare dake adawa da wani bangare wanda tsohuwar mataimakiyar shuagaban kasar madam Joice ke shugabanta, wadanda dukaninsu na kokowar kama madafun iko da kuma fatan gadon Mugabe, wanda zai cika shekaru 91 a watan Fabarairu mai tsayawa.

A makon da ya gabata, wani taron jam'iyyar dake mulkin kasar ta ZANU PF ya yi sanadiyyar wargaza bangaren da tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar ke jagoranta tare da haddasa sauke ta daga karagar mulkin kasar tare da aminanta guda 8. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China