Ministan yawon bude ido na kasar Zimbabwe, Walter Mzembi, ya bayyana cewa, gwamnatin kasarsa na shawarwari tare da hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin domin bullo da takardun Visa a nan gaba ga Sinawa masu yawon bude ido dake ziyartar kasar Zimbabwe. Mista Mzembi ya shaidawa manema labarai da jakadun kasashen waje a yayin wani dandali kan yawon bude ido a birnin Harare cewa, akwai wasu shirye shiryen da ake aiwatarwa a halin yanzu domin saukakawa 'yan kasar Sin samun takardun Visa da zaran zuwansu. A halin yanzu, ya kamata Sinawa su sami takardunsu na Visa na Zimbabwe kafin su yi tafiya. (Maman Ada)