A halin da ake ciki, shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya kara sallamar wasu yayan majalisar mulki ta kasar, ciki har da ministoci 2 da kuma mataimakan ministoci 5, a ci gaba da yake yi na garambawul a madafun iko na kasar wanda ya fara aiwatarwa a farkon watan Disamba.
Wata majiya ta kafofin watsa labarai na kasar ta ce, wata sanarwa daga ofishin Mugabe ta bayyana cewar, wadanda gwamnatin ta sallama daga mukamansu sun kai mutane 16, ciki har da minista dake gudanar da harkokin ofishin shugaban kasa, Flora Buka da kuma ministar dake kula da ofishin mataimakain shugaban kasa Sylvester Nguni, kana akwai mataimakan ministoci daga ma'aikatun lafiya, kwadago, albarkatun kasa, sufuri da shari'a.
Wannan garambawul ya biyo bayan wani dadadden fada da aka kasance ana yi a jam'iyyar ZANU-PF, a kwanan nan ne rashin jituwar ta yi kamari inda a karshen bangaren tsohuwar mataimakiyar shugaban kasa Joice Mujurum ya sha kashi bayan da a aka yi mata zargin wani yunkuri na kashe Mugabe, hakan ya sa an kori illahirin ministocin 7, dake mara mata baya.
A bisa dukkan alamu, abokin adawar tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar, ministan shari'a na Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ana ganin cewar shi ne ya yi nasara a kan tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar. (Suwaiba)