in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Mugabe ya gana da mamba a majalisar gudanarwar Sin
2015-02-10 10:27:42 cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi, ya gana da shugaba Robert Mugabe a birnin Harare, fadar gwamnatin Zimbabwe, a wani mataki na karfafa dangantakar Sin da nahiyar Afirka.

Da fari Mr. Yang ya taya shugaba Mugabe murnar kasancewa shugaban kungiyar AU na wannan karo, tare da kira gare shi da ya ba da tasa gudummawa, wajen bunkasa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Zimbabwe, da ma daukacin nahiyar Afirka baki daya.

Mr. Yang ya ce, akwai dadaddiyar dangantaka tsakanin kasar Sin da Zimbabwe, kuma kasarsa za ta ci gaba da daukar matakan karfafa wannan yanayi, ta yadda sassan biyu za su kai ga kara amincewa juna, da tallafawa juna, tare da cimma moriya tare.

A nasa tsokaci, shugaba Mugabe ya ce, kasarsa, za ta ci gaba da ba da hadin kai ga dangantakar dake tsakanin Sin da nahiyar Afirka. Ya ce, gwamnati da al'ummar kasarsa, na godiya game da irin tallafi da Sin ke bayarwa ga ci gaban Zimbabwe a fannoni da dama.

Bugu da kari shugaba Mugabe ya sha alwashin karfafa alakar dake tsakanin kasarsa da Sin, a dukkanin fannonin ci gaba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China