A jawabinsa shugaba Xi ya ce, duk da kalubalen da ake fuskanta a harkokin kasa da kasa da gagarumin aikin yayata manufofin kasar na yin gyare-gyare, kasar Sin da al'ummarta karkashin jagorancin JKS sun samu zaman lafiya da ci gaba cikin shekarun da suka gabata, baya ga nasarar da aka samu a bangaren yaki da cin hanci da rashawa.
A jawabinsa a madadin wadanda ba 'yan jam'iyyar ba, shugaban kwamitin tsakiya na jam'iyyar China Zhi Gong kana ministan kimiyya da fasahar kere-kere Wan Gang ya bayyana kudurinsu na ci gaba da taimakawa JKS wajen ganin an tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka tare da gina al'umma mai kyakkyawan makoma daga dukkan fannoni.
Cikin wadanda suka halarci ganawar sun hada da Yu Zhengsheng, shugaban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar Sin, mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Gaoli da kuma shugabannin jam'iyyun siyasa 8 wadanda ba su da alaka da JKS da kuma wakilan 'yan kasuwa da masana'antu. (Ibrahim)