Tare da kusantowar bikin bazara na gargajiya mafi muhimmanci ga Sinawa, al'ummar sinawa na cigaba da sayen kayayyaki don shirya wannan bikin. Kantuna da gidajen otel da dama sun fi samun ciniki a wannan muhimmin lokaci. Wani rahoton ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya nuna cewa, tun bayan da kwamitin tsakiya na JKS ya tsaida kuduri na 8 na tsimin kudi, an samu babban sauyi a kasuwannin sayen kayayyaki, yawan kayayyaki masu daraja da aka saya ya ragu, amma yawan kayayyakin masarufin da jama'a suka saya ya karu cikin sauri, ana kyautata zaton cewa, wannan dai zai kara karuwa a lokacin bikin bazara.
Bisa kididdigar ta hukumar kididdga ta Sin ta bayar, an ce, a shekara ta 2013, yawan kudin da ake kashewa a fannin abinci da abin sha a Sin ya gama zamaninsa na haura kashi 10 ko fiye bisa dari, karo na farko ne wannan adadi ya ragu kasa da kashi 10 bisa 100. Wani bincike na hukumomin jin ra'ayin jama'a ya nuna cewa, a bara masu kudi a kasar Sin sun rage yawan kudin da suka kashe da kashi 10 bisa dari, inda yawan raguwar kudin da aka kashe wajen sayen abubuwan kyaututuka ya kai kashi 25 bisa dari.
Game da yawan kudin da aka kashe kan kayayyakin yau da kullum, mataimakin ministan kasuwancin Sin Mista Fang Aiqing ya ce, ma'aikatarsa za ta ci gaba da kyautata tsari, da kara sa kaimi ga jama'a da su sayi kayayyaki, da kuma yin gyare gyare kan hanyoyin da ake bi a fannoni daban daban, don sa kaimi ga bunkasuwar sana'ar sayar da kayayyaki ga jama'a.(Danladi)