A gabanin zuwan bikin gargajiya mafi muhimmanci ga Sinawa wato bikin bazara, bisa binciken da cibiyar nazarin harkokin yawon shakatawa ta Sin ta yi, an ce, a lokacin bikin bazarar shekarar bana, karo na farko ne burin Sinawa na zuwa yawon shakatawa a ketare ya wuce na yawon shakatawa a cikin kasar Sin.
Wasu ma'aikatan hukumomin yawon shakatawa da kwararru sun yi nuni da cewa, a lokacin sanyi Sinawa suna son zabar tsibiran teku masu dumama, da sauran wurare masu ni'ima da ba su da sanyi domin yawon bude ido, kana a halin yanzu Sinawa da yawa su kan tafi ketare don yawon shakatawa.
An ce, tikitin zuwa tsibiran teku a lokacin bikin bazara an riga an sayar da dukkansu watanni biyu da suka gabata. Bisa kididdgar da cibiyar nazarin harkokin yawon shakatawa ta Sin ta yi an ce, a lokacin bikin bazara, yawan jama'ar kasar Sin da suka zabi yawo a ketare, ya wuce mutanen da suke yawo a gidan Sin a karo na farko. Yanzu haka, Korea ta Kudu, da Japan, da Singapoure, da Malaysia, da Thailand, da Amurka, da Faransa, da New Zealand, da Canada, da kuma Hongkong, Macau da Taiwan sun zama muhimman wuraren da Sinawa su kan zaba don yawon shakatawa.
Bisa alkaluman da muka samu daga hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta duniya, an ce, a kasashen Amurka, da Sin, da Jamus, da Britaniya, da Rasha aka fi samun jama'ar da ke yawon shakatawa a ketare. Kididdigar ta sheda cewa, a shekarar 2013, yawan Sinawa da suka yi yawo a ketare ya wuce miliyan 98, wanda ya karu da kashi 18% bisa na makamancin lokacin shekarar da ta gabata.(Danladi)