in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fitattaccen bikin bazarar Sinawa a kasashen waje na nuna al'adun sinawa masu sauki
2014-02-03 16:16:06 cri
Yadda bikin bazarar Sinawa yake kara yaduwa a kasashen waje yana kara bayyana saukin iko da kuma yadda ake kara fahimtar al'adun Sinawa, in ji jakadan kasar Sin dake Birtaniya Liu Xiaoming.

Mr. Liu a cikin hirar da ya yi da Xinhua a ranar Lahadin nan a birnin London, ya ce al'adun Sinawa yana nuna saukin ikon kasar Sin, sannan bikin bazarar na sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa ta taimaka wajen zurfafa mutunci da fahimtar juna tsakanin al'ummar Sinawa da sauran jama'ar duniya.

Jakadan kasar Sin wanda yake bayani game da gaggarumin bikin da aka yi a birnin na London na farawar sabuwar shekarar Sinawa wanda ya samu halarta kusan mutane 500,000, ya ce al'adun Sinawa yana kara samun karbuwa a kasashen waje wanda hakan kadai ya isa ya nuna ci gaban da kasar Sin ta samu wajen nuna ma sauran al'ummar duniya yadda take. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China