in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A Najeriya INEC na hadin gwiwa da hukumar NCAC domin wayar da kan masu zabe
2015-02-07 16:32:29 cri
A wani mataki na tabbatar da nasarar aikin raba katunan zabe na dindindin da hukumar zaben Najeriya INEC ke gudanarwa, hukumar ta fara wani shiri na hadin gwiwa da hukumar mai kula da harkokin al'adu a kasar NCAC.

Shirin wanda ya kunshi amfani da wasannin kwaikwayo wajen ilmantar da al'ummar kasar alfanun dake tattare da karbar katin zaben, zai game rassan hukumar ta NCAC dake daukacin jihohin kasar.

Da yake karin haske game da hakan, yayin taron karawa juna sani na hadin gwiwar hukumonin biyu, wanda ya gudana a birnin Abuja, kwamishina mai lura da harkar raba katunan zabe Dr. Chris O. Iyimoga, ya ce INEC ta yi amanna da tasirin wannan tsari a fannin yada bayanai, da wayar da kan jama'a game da muhimmancin gudanar zabe lami-lafiya, baya ga kasancewar hakan wata hanya ta yada al'adun al'ummar kasar.

A nata tsokaci kuwa, babbar darakta a hukumar NCAC, uwargida Dayo Keshi, cewa ta yi hukumarta za ta bi hanyoyin duk da suka wajaba, domin tabbatar da nasarar wannan hadin gwiwa, ta na mai cewa NCACn ta shirya tsaf, domin tabbatar da bada gudummawa, wajen ganin an gudanar da babban zaben Najeriyar cikin kyakkyawan yanayi.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China