Ganawar da ake sa ran Shugaba Goodluck Jonathan zai shugabanta zai kuma duba shirye shiryen da hukumar zabe mai zaman kanta ta yi a kan babban zaben da kuma na bangaren tsaro.
Wadansu daga cikin matsalolin dake kunno kai na zaben shi ne rashin kammala rarraba katunan zabe ga jama'a da hukumar zabe tayi, sai dai hukumar zaben a nata bangaren tace babu gudu babu ja da baya a game da ranar da ta tsaida na zabukan kasar.