in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata jami'iyyar siyasa a Nigeriya ta tsaida Goodluck Jonthan a dan takarar ta
2015-02-04 20:38:36 cri
Wata jam'iyyar siyasa a Nigeriya SDP ta tsaida shugaban kasa mai ci yanzu na jami'iyyar PDP a matsayin nata dan takarar a babban zaben dake tafe ranar 14 ga watan Fabrairu.

Jami'iyyar ta cimma wannan matsaya ne sakamakon rahoton da kwamitin da ta kafa akan fidda dan takara, inji kakakin jam'iyar Abdul Isiaq a Abuja babban birnin kasar.

Babban shugaban jam'iyyar Olu Falae ya nuna alamun gazawar jam'iyar na tsaida dan takarar shugaban kasa wanda ya sa aka cimma wannan matsaya.

Abdul Isiaq yace kwamitin, a cikin rahotonsa ga shuagaban jam'iyyar ta yanke shawarar hakan ne ganin cewa dukkan sauran 'yan takarar jami'yyun kasa babu wanda ya nemi goyon bayanta in banda Shugaban Nigeriya mai ci yanzu Goodluck Jonathan.

Yace kwamitin ya lura cewa PDP ta amince da sharuddan da jami'iyar ta SDP ta gabatar idan har ana son goyon bayanta.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China