Kasar Benin ta sami matsayi na 13 a cikin kasashen Afrika 47 da kungiyar yaki da cin hanci ta duniya ta yi bincike kan su a shekarar 2014, a cewar wani rahoto na kungiyar da aka ta fitar a ranar Laraba.
A cikin kasashe 175 da binciken ya shafa, kasar Benin na matsayi na 80 a duniya tare da maki 39 bisa 100, inda a shekarar 2013, kasar ta rike matsayi na 94 a cikin kasashe 177 da binciken ya shafa.
A cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya yi da 'yan kasar Benin a matakai daban daban, dukkansu suna imanin cewa, matakan gwamnatin kasar ta dauka ne wajen yaki da cin hanci a kasar suka taimakawa kasar Benin samun wannan matsayi.
Tun lokacin zuwa shugaban kasar Benin Boni Yayi a kan karagar mulki a shekarar 2006, gwamnatin kasar ta kafa wata babbar hukumar bincike ta kasa, da kuma wata cibiya guda dake kula da dukkan harkokin kwastan wanda ya hada da shigar da internet a cikin aikin kwastan, tashoshin bincike, hukumomin tashoshin bakin ruwa da sauran wasu ayyuka, a cikin tashar ruwan Cotonou.
Baya ga wadannan matakai, gwamnatin kasar Benin ta aiwatar da wasu jerin sauye-sauye, ta hanyar cimma wata dokar yaki da cin hanci da karbar rashawa, da kuma bunkasa sauye-sauye a cikin ma'aikatun gwamnati da hukumomin kasa. (Maman Ada)