Majalissar dokokin kasar Algeriya ta amince da dokar da ta shafi yaki da halaltar da kazamin kudi da kuma hana duk wani yunkuri da zai samar da kudi ga 'yan ta'adda.
Dokar ta kara karfafa matsayin kasar da inganta kokarinta game da yakar ta'addanci ta hanyar toshe duk wata kafa da 'yan ta'addan za su samu kudin aiwatar da ayyukansu, in ji ministan shari'a Tayeb Louh lokacin da yake bayani ga manema labarai bayan da majalissar wakilan kasar sun amince da dokar.
Wannan doka ta ba da damar tantance aikin da zai zama laifi ana samar da kudade ne ga kungiyoyin ta'addancin, sannan ta fito da dokar yaki da ta'addancin na cikin gida, ta yadda za ta tafi da tsarin kasashen duniya baki daya.
A yadda sabuwar dokar ta bayyana samar da kudade ga 'yan ta'adda, ana kallon shi a wani laifi ko da kuwa yadda aka yi musayar kudin ba ta hanyar ta'addanci ba ne, in ji miinistan.
Dokar ta kuma ba da shawarar fadada karfin kotuna a game da laifukan da suka shafi samar da kudade ga ta'addanci da almundahanar kudi da suka hada da wanda aka yi a a kasashen waje domin al'ummar Algeriyan.
A wata sabuwa kuma, dokar ta ba da dama ga alkali ya daskarar da kudaden da aka yi niyyar amfani da su don taimaka wa ta'addanci.
Wannan doka dai za'a duba ta, sannan majalissar dattawar kasar za ta amince da ita kafin a mayar wa majalissar zartarwar kasar ta daukaka kafin a fara aiki da ita daga karshe. (Fatimah)