in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na fatan shekarar 2015 za ta kasance shekarar raya muradun shekarar 2063
2015-01-30 16:38:10 cri


An bude taron koli karo na 24 na kungiyar tarrayar Afrika AU a ranar Juma'ar nan, a birnin Addis Ababa hedkwatar kasar Habasha, taron da ya maida bunkasa rayuwar 'ya'ya mata matukar muhimmanci cikin manufofin raya nahiyar Afrika.

Wannan dai manufa na cikin jigon taron na bana, kuma ta kasance daya daga manyan kudurorin ci gaban nahiyar da ake fatan cimma nasarar su nan da shekarar 2063.

Yayin bude taron na yini biyu, shugabanni, da wakilai daga kasashe mambobin AU kimanin 50, sun tattauna kan tsarin raya Afrika cikin dogon lokaci, da batun rigakafi da na shawo kan cutar Ebola, da yanayin da ake ciki a yankunan da ake fama da cutar. Sauran batutuwan sun hada da na yaki da ta'addanci, da samun bunkasuwa tare, da kiyaye muhalli da sauransu.

A matsayin AU na kungiyar hadin kan daukacin kasashen nahiyar Afrika, wadda kuma ke sa ido ga harkokin siyasa, da tattalin arziki, da aikin soja da sauransu, AU na kuma kokarin kafa sabuwar Afrika mai cike da hadin gwiwa, da yunkurin kaiwa ga matsaya daya tsakanin mambobin ta kan wasu manyan batutuwan duniya.

Taron kolin babbar hukumar kungiyar, wanda a baya a kan kira a ko wace shekara, daga shekarar 2005 an maida shi sau biyu a ko wace shekara, inda daya ke gudana a hedkwatar kungiyar, yayin da kuma ake gudanar da dayan a daya daga kasashe mambobin kungiyar.

A kuma kowane karo a kan ayyana wani jigo a matsayin taken taron. Jigon taron na wannan karo shi ne "Baiwa 'ya'ya mata hakkinsu, da raya Afrika" bisa kudurin ci gaba da ake fatan cimma nan da shekarar 2063.

Hakan ya sa wannan shekara ta 2015, ta kasance shekarar tabbatar da hakkin 'ya'ya mata ta AU. Kana kudurin shekarar 2063 na kunshe da kiran da shugabannin AUn suka yi a shekarar 2013, don tsaida tafarki, da matakan raya Afrika cikin shekaru 50 masu zuwa, ko muradin 2063.

Cikin jawabinta, shugabar AU Nkosazana Dlamini Zuma ta bayyana cewa, dalilin da ya sa aka maida wannan shekara ta bana ta kasance shekarar baiwa 'ya'ya mata hakkinsu shi ne, kasancewar Afrika na matukar bukatar warware batun matsayin 'ya'ya mata, da ragowar batutuwa, a sa'i daya kuma, mata na da rawar takawa game da raya Afrika.

Bisa kididdigar da asusun kula da yawan al'umma na MDD ya bayar, an ce, mata masu juna biyu fiye da dubu 180 ne ke mutuwa a kowace shekara, sakamakon kasa samun jiyyar da ta dace a wasu kasashen dake kudu da Sahara. Ban da wannan kuma, ana yi wa 'ya'ya mata dake tsakanin shekarunsu 4 zuwa 12 kimanin miliyan 2 kaciya, matakin da a cewar asusun na haifarwa yaran babbar matsala.

Yayin taro na wannan karo, wakilai daban-daban daga MDD, da sauransu kungiyoyin kasa da kasa za su tattauna kan yadda za a kiyaye 'ya'ya mata daga cin zarafi, da kiyaye hakkokinsu da dai sauran batutuwa masu alaka da hakan.

Ban da haka kuma, wannan shekarar kasancewarta, ta cika shekaru 20 da gudanar babban taro game da rayuwar 'ya'ya mata na duniya da ya gudana a birnin Beijing, hukumar kare hakkin mata ta MDD ta aiwatar da manufar tunawa da wannan batu, domin jan hankulan bangarorin daban-daban, su dauki matakan da suka dace, na tabbatar da aiwatar da sanarwar Beijing, da kuma manyan ka'idojinta.

Madam Zuma ta yi fatan bangarori daban-daban za su dauki matakan da suka dace, su kuma yi iyakacin kokarin tabbatar da wannan buri, ta yin amfani da wannan zarafi mai kyau. Ta kuma yi fatan za a share fage ga taron 'ya'ya mata na kasa da kasa, wanda za a yi a hedkwatar MDD dake birnin New York a cikin watan Maris mai zuwa.

Yayin taron kolin ko wane karo dai, ban da tabbatar da jigonsa, raya Afrika cikin dogon lokaci, shi ma ya zama wani babban jigo da babu shakka za a tattauna shi, kuma za a mai da hankali kan wasu manyan batutuwa dake jawo hankalin kasa da kasa a halin yanzu.

Ko da yake, taron koli zai gudana ne cikin kwanaki biyu kacal, duk da haka shugabanni, da wakilan AU sun fara tattauna kan wasu batutuwa iri daban-daban, mako daya kafin babban taron.

Baya ga batun baiwa 'ya'ya mata hakkinsu, za a kuma maida hankali sosai kan wasu manyan batutuwa, ciki hadda yadda za a tabbatar da muradun shekarar 2063, da tabbatar da yankin bai daya bisa ajandar taron, da raya Afrika cikin lumana da wadata da sauransu.

Game da batun shawo kan cutar Ebola kuwa, shugabanni mahalartan taron, za su yi musayar ra'ayi game da kafa wata cibiyar rigakafin cututtuka a nahiyar ta Afrika. Ban da haka kuma, za a tattauna kan aikin yaki da ta'addanci, da tsaron wasu kasashe, ciki hadda Najeriya, da Somaliya, da Afrika ta Tsakiya, da Mali da Kamaru, da Sudan ta Kudu da sauransu, da kuma yadda za a aiwatar da hadin gwiwa, wajen yaki da ta'addanci, da kafa wata rundunar aikin ko-ta-kwana a Afirka, batutuwan da za su kasance manya a yayin tattaunar ta wannan karo.

Rahotanni sun bayyana cewa, kafin bude taron na wannan karo, hukumomin AU sun kulla yarjeniyoyi dangane da wasu manyan batutuwa. Shugaba Zuma da manzon musamman na gwamnatin kasar Sin, kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Ming, sun rattaba hannu kan wata takardar fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu, game da sa kaimi da hadin gwiwa ga bunkasar harkokin sufuri, da samar da ababen more rayuwa a nahiyar Afrika. Dadin dadawa, wasu hukumomin AUn sun tattauna kan wasu manyan batutuwa, ciki hadda daga matsayin mata cikin gwamnatoci, da hana aure ga kananan yara, da kara zuba jari ga aikin gona, da kawar da talauci, da kara horar da 'yan kwadago da sauransu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China