in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta kira taron gaggawa a kan Ebola
2014-09-09 17:16:06 cri

A ranar 8 ga watan nan ne kwamitin zartaswa na kungiyar hadin kan Afirka AU, ya kira wani taron gaggawa a hedkwatar kungiyar da ke birnin Addis Ababan kasar Habasha, inda aka yi kira ga mambobin kungiyar da su hada kai wajen yaki da cutar Ebola da ke addabar wasu kasashen dake yammacin Afirka, a sa'i daya kuma aka bukaci gamayyar kasa da kasa da su samar da karin gudummawa a wannan fanni.

Burin da ake neman cimmawa a wajen taron shi ne, fatan ganin kasashen Afirka sun dauki matsayi na bai daya, da kuma manufofin da suka cancanta a aikin da ake yi na yaki da cutar Ebola. Ban da haka, taron zai kuma duba yiwuwar ko za a dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa kasashen da abin ya shafa, da ma kangiyar da aka iya yi wa tashar jiragen ruwa, da iyakokin kasashen ko a'a, musamman sakamakon yadda matakan ke lalata sunan kasashen da kuma al'ummarsu.

A gun taron, shugabar hukumar kungiyar tarayyar Afirka Nkosazana Dlamini-Zuma ta bayyana cewa, ya zama dole a dauki matakai na bai daya kan mutanen da cutar ta Ebola ta shafa don ba su gudummawa.

Madam Zuma ta kuma yi kira ga kafofin yada labarai na Afirka, da kungiyoyin jama'a, da masu harkokin da suka shafi al'adu, da jam'iyyun siyasa, da ma hukumomi, da su hada kai da gwamnatocin kasa da kasa da na tattalin arziki na shiyya shiyya, da kuma kungiyar tarayyar Afirka. Kana an bukaci sassan su maida batun yada sahihan bayanan da suka shafi cutar Ebola, a matsayin wani bangare na aikin yaki da cutar, don fadakar da al'ummar Afirka, hanyoyin yaduwar cutar, da yadda za a kula da masu fama da ita da kuma jana'izarsu. Ban da haka, ta kuma yi kira ga masana kimiyya da su rubanya kokarinsu wajen kirkiro magungunan cutar Ebola.

A cewar madam Zuma, kungiyar tarayyar Afirka ta damu game da yadda kasashen Guinea da Saliyo da Liberia za su farfado daga cutar Ebola, musamman ta fannonin cinikin ketare, da samar da isashen abinci, da guraben aikin yi da kuma hauhawar farashin abinci. Ta ce, kamata ya yi a dauki tsauraran matakai na hana yaduwar cutar, haka kuma a sa'i daya, ya zama dole a dauki matakan bunkasa aikin gona, da harkokin kasuwanci, tare kuma da mai da hankali kan tasirin da cutar take yi ga mata.

A kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa yanzu, kashi 60% na mutanen da suka kamu da Ebola ko suka mutu a sanadiyyar cutar mata ne, musamman ma nas nas da kuma masu aikin share-share da masu wanke tufafi da sauransu.

A ra'ayin kwamitin kula da tattalin arzikin Afirka na MDD, cutar Ebola ta haifar da illoli game da aikin hakar ma'adinai, da aikin gona, da cinikayyar cikin gida da ta ketare, da zirga-zirgar jiragen sama da zuba jari, wadanda suka kasance muhimman fannonin tattalin arziki, matakin da ke nuni da cewa jimillar GDP na kasashen Guinea da Saliyo da Liberia na iya faduwa. Don haka, mataimakin babban magatakardan MDD, kana shugaban zartaswa na kwamitin kula da tattalin arzikin MDD Carlos Lopes ya bukaci jama'ar Afirka, da kada su yi kasa-a-gwiwa a irin wannan yanayi na musamman, a maimakon haka kamata ya yi su tashi tsaye wajen yaki da cutar.

Har wa yau, shi ma a nasa bangare mataimakin babban darektan bankin raya Afirka ya jaddada tasirin da Ebola ke haifarwa, inda ya jaddada tasirin dadewar ta, da karin illolin da za ta iya kawo wa tattalin arziki da zamantakewar al'umma.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China