in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu ci gaba game da kyautata zaman rayuwar jama'a a kasar Sin
2015-01-30 16:18:26 cri
Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya gudanar da taron manema labaru kan yanayin zaman rayuwar jama'ar kasar a Juma'ar nan, inda shugabannin ma'aikatar ba da ilmi, da na ma'aikatar harkokin jama'a, da ofishin taimakawa masu fama da talauci na majalisar gudanarwar kasar, suka yi bayani game da halin da ake ciki game da zamantakewar jama'ar kasar a shekarar 2014, tare da amsa tambayoyi daga 'yan jarida.

A cikin watan Oktobar bara ne dai majalissar gudanarwar kasar Sin, ta gabatar da wata takarda, mai kunshe da shirin kafa wani tsari na ba da taimako a dukkan fannoni.

Game da hakan mataimakin ministan harkokin jama'a Dou Yupei, ya yi nuni da cewa, za a yi kokarin fadada wuraren da ake samar da taimako, da daga ma'aunin ba da taimako, kana za a yi kokarin samun ci gaba wajen samar da sauki ga jama'a a fannin neman taimako.

Game da shirin kyautata lafiyar daliban makarantun firamare da na midil dake kauyukan kasar Sin kuwa, mataimakiyar ministan ilimi ta kasar Lu Xi, ta bayyana cewa yawan kudin da Sin ta zuba kan shirin daga shekarar 2011 zuwa yanzu, ya kai Yuan biliyan 47.2. Kaza lika bisa binciken da aka yi, tallafin ya ba da damar kyautata lafiyar dalibai, da 'yancin su na samun managarcin ilimi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China