Kasar Chadi a ranar Litinin din nan ta karbi shugabancin kwamitin tsaro na MDD na watan Disamba. Cherif Mahamat Zene, wakilin din din din na kasar a majalissar ya karbi shugabancin kwamitin ne ake yi zagaye zagaye daga wajen Gary Quinlan, jakadan kasar Australiya a majalissar wanda ya rike kujerar a watan Nuwamba.
A matsayin kasar da ba ta da kujerar din din din a kwamitin, Chadi ta fara wa'adinta na shekaru biyu a kwamitin mai wakilai 15 a ranar 1 ga watan Janairun wannan shekarar ta 2014.
Kamar yadda tsarin majalissar yake, kwamitin tsaron ke da nauyin tafiyar da ayyukan zaman lafiya da tsaro a duniya baki daya, yana da wakilan din din din guda 5 da suka hada da kasashen Sin, Amurka, Britaniya, Faransa da Rasha. Sai kuma wakilai da ba na din din din ba guda 10 da aka zabe daga shekaru 2 zuwa 5.
Shugabancin kwamitin, ana yin shi ne zagaye zagaye a tsakanin kasashen dake cikin kwamitin tsaro da wanzar da zaman lafiya duk wata, bisa farkon kalmar sunan kasa a haruffan Turanci. (Fatimah)