in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana shirin kafa cibiyar Afrika kan fasahohin sadarwa a N'Djamena
2014-09-10 10:39:34 cri

Za'a kafa wata cibiyar Afrika kan fasahohin zamani na sadarwa CATI a cikin 'yan shekaru masu zuwa a N'Djamena, babban birnin kasar Chadi, inda kuma za ta kasance wata cibiya ga matasan Afrika domin bunkasa kirkire-kirkire, kago sabbin abubuwa da shirye-shirye a bangaren harkokin sadarwa na TIC, da na rediyo da talabijin, in ji shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno.

CATI, wani babban shiri ne na Afrika kan rediyo da talabijin na zamani a doron kasa, da 'yan Afrika suka tsara domin 'yan Afrika, kuma zai kasance wani kokarin Chadi wajen aiwatar da tsarin NEPAD dake ba da fifiko ga samar da labarai na tushe masu nagarta, da aka tantance cikin nuna hotunan gaskiya da bayyana wata Afrika mai tashi tsaye da samun cigaba, in ji shugaban kasar Chadi a cikin wani jawabinsa a yayin bikin bude dandalin kasa da kasa kan harkokin sadarwa na TIC.

Za'a gina CATI a cikin ginin cibiyar harkokin kasa da kasa da ake cikin ginawa a tsakiyar birnin N'Djamena domin babban taron kungiyar tarayyar Afrika AU na gaba, kuma zai kasance wani ginin zamani dake dacewa wajen gudanar da ayyukan da suka hada da nazari, bincike, bajen koli, taron karawa juna sani, da kuma musanya a fannoni daban daban domin cigaban ma'aikatu da wasu kere-kere a bangaren harkokin sadarwa na TIC.

Haka kuma, shugaba Deby Itno ya bayyana tsinkayensa na maida birnin N'Djamena, a wata cibiyar harkokin sadarwa na TIC a nahiyar Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China