Daidai kamar muhimmancin bikin kirsimati ga Turawa, bikin bazara ya zama biki mafi girma ga Sinawa daga cikin bukukuwan duk shekara. Ko da yake bisa sauye-sauyen zamani, aikace-aikacen da ake yi a gun bikin bazara suna ta canjawa, hanyoyin da mutanen ke bi don yin biki kuma suna ta canjawa, amma har ila yau matsayin bikin bazara da ke cikin zaman rayuwa da tunanin Sinawa ba za a iya yi mishi tashi-in-maye ba. An ce, bikin bazara na kasar Sin yana da tarihin da ya shafe shekaru 4000...(Cikakke)
Bisa al'adar jama'ar kasar Sin, a kan ce bikin bazara ya fara daga ran 23 ga watan Disamba na kalandar gargajiya ta kasar, kuma ya dade har zuwa bikin Yuanxiao na ran 15 ga watan farko na sabuwar shekara, wato duk tsawon bikin ya kai wajen makonni 3. Cikin wannan lokaci, kwana daya da yini daya wato jajibirin sabuwar shekara na ran 30 ga watan Disamba da dare da ran 1 ga watan farko su ne suka fi kasaita, ana iya cewa su ne wani tashe na bikin bazara. Domin marabtar bikin bazara...(Cikakke)
A wurare daban-daban na kasar Sin, mutane suna da al'adun gargajiya iri daban-daban wajen yin bikin bazara, amma ko a arewaci ko kuma a kudancin kasar duk 'yan iyali sukan hadu don cin abinci tare a jajibirin bikin da dare, wannan ya zama wani wajibabbun abubuwa ne. A kudancin kasar, abincin nan yakan hada da nama da ganyaye wadanda yawan irinsu ya kai fiye da 10, daga cikinsu tilas ne da akwai irin abincin da ake kira Tofu wanda aka yi da wake da kuma "Yu" wato kifi, dalilin da ya sa aka yi haka shi ne sabo da kalmar "Fuyu"...(Cikakke)
Manna takardun waka kwar biyu da zane-zane na sabuwar shekara, da kunna wutar fitilu masu launi, su ma aikace-aikace ne da ake yi domin murnar bikin bazara. A lokacin bikin, kasuwanni sukan sayar da zane-zane na sabuwar shekara da takardun waka kwar biyu iri daban-daban wadanda ke bayyana zaman jin dadin jama'a da ayyukan da suke yi cikin fara'a, wadannan kuma aka bar su don a zaba. Taron nune-nunen fitilu da aka yi a gun bikin bazara shi ma wani biki ne mai ban sha'awa kwarai...(Cikakke)

Not Found!(404)

• 'Yan kasar Birtaniya sun murnar shiga sabuwar shekara ta Sinawa a birnin London 2015-02-23
• Ana murnar shiga sabuwar shekara ta Sinawa a birnin London na kasar Birtaniya 2015-02-23
• Birnin Sao Paulo a Brazil sun yi bikin sabuwar shekarar Sinawa ta gargajiya 2015-02-22
• An samu karuwar tafiye-tafiye a lokutan hutu a Sin 2015-02-19
• Shugabannin kasa da kasa sun mika sakon murnar sabuwar shekara ga kasar Sin 2015-02-19
More>>
More>>
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China