in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Share fagen bikin bazarar Sinawa
2013-02-07 15:35:03 cri

Bisa al'adar jama'ar kasar Sin, a kan ce bikin bazara ya fara daga ran 23 ga watan Disamba na kalandar gargajiya ta kasar, kuma ya dade har zuwa bikin Yuanxiao na ran 15 ga watan farko na sabuwar shekara, wato duk tsawon bikin ya kai wajen makonni 3. Cikin wannan lokaci, kwana daya da yini daya wato jajibirin sabuwar shekara na ran 30 ga watan Disamba da dare da ran 1 ga watan farko su ne suka fi kasaita, ana iya cewa su ne wani tashe na bikin bazara. Domin marabtar bikin bazara, daga birane zuwa kauyuka, mutane suna ta yin ayyuka daban-daban domin shirin bikin. A kauyuka, tun da aka shiga cikin watan Disamba na kalandar kasar Sin, sai a fara ayyukan share fage domin bikin, iyalan manoma da yawa sukan share daki, da wanke tufafi da barguna domin kau da rubabbun abubuwa ta yadda za a samu sabon halin zama. 'Yan iyali kuma sun yi ta sayen kayayyaki iri-iri daga kasuwa domin bikin bazara, kamar alewa da kayan zaki da nama da 'ya'yan itatuwa, ta yadda za su samu isashen abinci domin kansu kuma domin karbar baki a lokacin bikin. A manyan birane kuma, an fara ayyukan share fage tun tuni domin bikin, sassan al'adu da kungiyoyin 'yan fasaha sukan shirya wasanni da yawa masu ban sha'awa, gidajen rediyo mai hoto kuma sukan yi shirye-shirye iri daban-daban, ban da wannan kuma a kan shirya baje-koli cikin manyan lambunan shan iska daban- daban, ta yadda mutane masu yawon shakatawa za su iya yin shagulgula masu nishadi wadanda yawansu ba a zo a gani ba ne, manyan kantuna kuma su kan yi odar hajjoji daga wurare daban- daban na duk kasa baki daya har ma daga kasashen waje domin biyan bukatun 'yan birni a gun bikin bazara. An taba yin kididdigar cewa, yawan kudin da Sinawa suka kashe domin sayen kayayyaki a lokacin bikin bazara ya kai sulusi har ma ya wuce haka bisa na duk shekarar.(Umaru)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China