An ce, bikin bazara na kasar Sin yana da tarihin da ya shafe shekaru 4000, amma a farkon lokaci ba a kiransa bikin bazara, kuma ba a tsai da ranar bikin ba. Zuwa shekara ta 2000 da wani abu na kafin haifuwar Annabi Isa Alaihisallam, a wancan lokaci mutane sun dauki tsawon lokacin juyawar tauraron da ake kira Jupiter sau daya ta zama "Sui" daya, kuma akan kira bikin bazara da sunan "Sui". Kafin shekarar 1000 na kafin haifuwar annabi Isa Alaihisallam, mutane sun ba wa bikin bazara da sunan "Nian". A wancan lokaci kuwa, kalmar "Nian" tana da ma'anar samun amfanin gona mai armashi ne, idan an samu amfanin gona mai armashi, sai a ce "akwai babban Nian".(Umaru)