in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jajibirin sabuwar shekara
2013-02-07 15:37:39 cri

A wurare daban-daban na kasar Sin, mutane suna da al'adun gargajiya iri daban-daban wajen yin bikin bazara, amma ko a arewaci ko kuma a kudancin kasar duk 'yan iyali sukan hadu don cin abinci tare a jajibirin bikin da dare, wannan ya zama wani wajibabbun abubuwa ne. A kudancin kasar, abincin nan yakan hada da nama da ganyaye wadanda yawan irinsu ya kai fiye da 10, daga cikinsu tilas ne da akwai irin abincin da ake kira Tofu wanda aka yi da wake, da kuma "Yu" wato kifi, dalilin da ya sa aka yi haka shi ne sabo da kalmar "Fuyu" wadda lafazinta cikin Sinanci ya yi daidai da na kalmar "arziki". A arewancin kasar kuma, yawancin iyalai sukan ci irin abincin da ake kira Jiaozi a jabibiri da dare, 'yan iyali daya dukkansu suna yi Jiaozi tare, irin wannan abinci an yi shi ne ta hanyar kunsa daddatsattsen nama mai dadin ci cikin kullin garin alkama mai da'ira, kuma an dafa su cikin tafasassen ruwa, kuma an ci Jiaozi tare da kayan yaji, duk 'yan iyali suna zaune a kewayen tebur suna cin Jiaozi tare cikin halin annashuwa.

A jajibiri da dare, mutane su kan tsayawa ba su yi barci, suna yin wasanni iri-iri cikin murma da fara har duk dare, an yi haka ne domin wucewar tsohuwar shekara da shiga cikin sabuwar shekara. A lokacin zuwan sabuwar shekara, mutane su kan harba wutar gimbiya domin murnar bikin. Ana bin wannan al'ada ce domin kaucewa miyagun shaidanu. A safiyar rana ta farko ta sabuwar shekara, duk 'yan iyali manya da kanana sukan ci ado da tufaffin ranar biki, kuma sun fara karbar baki ko sun fita waje don yi wa mutane barka da sabuwar shekara. Lokacin da ake ganawa da juna, su kan ce "barka da sabuwar shekara", da "barka da bikin bazara" da sauran kalmomi masu kawo alheri domin nuna wa juna girmamawa, daga baya kuma sun koma gida sun sha alewa da 'ya'yan itatuwa, kuma suna shan ti suna yin zantakayya kan harkokin gida. Idan an yi sabani cikin shekarar da ta wuce a tsakanin dangogi da aminai, amma muddin sun yi wa juna bakunci a gun bikin bazara domin barka da sabuwar shekara, sai a ce sun kai fahimtar juna ke nan. (Umaru)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China