in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Equatorial Guinea ta sake yin kunnen doki a gasar AFCON na bana
2015-01-22 09:25:24 cri

A jiya ne kasar Equatorial Guinea da ke daukar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen nahiyar Afrika na shekarar 2015 (AFCON) suka tashi babu ci a wasan da suka kara da kasar Burkina Faso a wasan da suka buga a filin wasa na Bata.

Bayan kunnen doki na ci 1 da 1 a wasanta na farko da ta buga da Congo Brazzaville, yanzu haka kasar Equatorial Guinea tana da maki biyu, yayin da Burkina Faso ke kasancewa ta karshe a rukunin na daya (A) da maki daya tak bayan kashin da ta sha a hannun Gabon da ci 2 da nema. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China