Kulaf din kwallon kafar kasar Burkina Faso, na fatan farfadowa bayan rashin nasarar da ya samu a wasan farko da ya buga, a ci gaba da buga gasar cin kofin nahiyar Afirka AFCON dake gudana yanzu haka a Equatorial Guinea.
A cewar kocin kungiyar Paul Put, sun gano kurakuran da suka sanya kasar Gabon zura musu kwallaye har 2 a raga, yayin wasan farko da suka buga a rukunin A, kuma za su yi gyara domin kaucewa sake aukuwar hakan.
Yanzu haka dai Burkina Faso wadda ta zamo ta biyu a gasar da ta gabata a shekarar 2013, za ta buga wasanta na biyu a Larabar nan ne da mai masaukin baki wato Equatorial Guinea.
A daya hannun kuma kocin Equatorial Guinea Esteban Becker, ya shaida wa manema labaru cewa, 'yan wasansa sun shirya tsaf, don ganin sun doke Brukina Faso a wasan na yau. (Saminu)