A jiya ne mai horas da 'yan wasan kasar Ghana, kana tsohon kociyan kulob din Chelsea Avrant Grant ya fara wasansa a gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afirka AFCON na shekara 2015 da rashin sa'a, bayan da kasar Senegal ta doke ta da ci 2 da 1 a wasan farko na rukuni na uku (C) da suka fafata a filin wasa na Mongomo da ke kasar Equatorial Guinea.
Kasar Ghana ce ta fara zura kwallo ta hannun kyaftin dinta da ke wasa a kasar Faransa Andre Ayew a minti na 12 da fara wasa ta hanyar bugun daga kai, sai mai tsaron gida, yayin da Senegal ta samu nata kwallayen ta hannun 'yan wasanninta Mame Biram Diouf da Moussa Sow, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci. Wannan shi ne karo na farko da kasar ta Senegal ta doke kasar Ghana a wannan gasa.
Ghana dai ta ci gaba da mamaye wasan, amma haka aka tashi wasan Senegal na da ci 2, Ghana na da kwallo 1 a raga. (Ibrahim)