Hukumar kula da kwallon kafar kasar Equatorial Guinea, ta mika wata takardar korafi ga hukumar AFCON, tana mai kalubalantar kwallon da aka soke mata, yayin wasanta da kasar Congo Brazzaville.
Bisa sakamakon wasan da kasashen biyu suka buga a ranar Asabar, an tashi ne kunnen doki ne 1 da 1, bayan da alkalin wasan ya hana wata kwallon ta daban, da Equatorial Guinea ta jefa a ragar Congo Brazzaville.
A cewar wani jami'in hukumar watsa labarun kasar ta Equatorial Guinea David Monsuy, kasarsa na kallon soke wannan kwallo a matsayin rashin adalci, wanda ka iya hana ta samun cikakkiyar nasara a gasar. Don haka nema suka ga dacewar gabatar da koken nasu, ga hukumar ta AFCON, wadda ke shirya gasar domin daukar matakin da ya dace. (Saminu)