Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, gwamnati za ta kara tallafi kudin da ta ke baiwa kamfanonin kasar da ke harkokin zuba jari da wasu ayyuka a sassa daban-daban na duniya.
Li wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan taron majalisar zartarwar kasar da ya jagoranta ya ce, matakin zai taimaka wajen kara yawan kayayyakin da kamfanonin ke samarwa baya ga kara dankon zumunci tsakanin kamfanonin da ke kasashen waje.
Bugu da kari matakin zai kuma kara haifar da takara tsakanin kayayyaki kirar kasar Sin, musamman manyan na'urori, daga darajar cinikayyar ketara, da kuma daga matsayin masana'antun samar da kayayyaki da hukumomin kudi.
Bisa wannan tsarin, kasar Sin za ta inganta manufofin da suka shafi biyan kudade a harkokin ketare, da rancen kudaden fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje da bankuna ke bayarwa. (Ibrahim)