Yan takarar kujerar shugabancin Najeriya sun amince da wata yarjejeniya, wadda ta tanaji kaucewa furta kalai masu iya harzuka jama'a, a yayin yakin neman zabe, da ma bayan babban zaben kasar dake tafe cikin wata mai zuwa.
Shugaban kasar mai ci Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP, da 'dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta APC Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, da wasu sauran 'yan takara 10 ne suka rattabata hannu kan wannan yarjejeniya a jiya Laraba.
Rahotanni sun bayyana cewa, hakan wani mataki ne da 'yan takarar suka dauka domin kaucewa aukuwar tashe-tashen hankula masu alaka da manyan zabukan kasar, tare da burin su na martaba tanaje-tanaje dake kudin mulkin tarayyar Najeriyar.
Yarjejeniyar ta kuma kunshi kudurin 'yan takarar na daukar dukkanin matakai, da ka iya taimakawa hadin kan 'yan kasar. Kaza lika sun amince da marawa manufofin ci gaban kasar baya, samar da duk wasu bukatu na kashin kan su. Baya ga biyayya ga daukacin dokokin zabe kamar yadda doka ta tanada.
Bugu da kari 'yan takarar sun yi kira ga daukacin hukumomin kasar da su kasance masu gaskiya da amana, domin cimma burin da aka sanya gaba. (Saminu)