in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar PDP a Najeriya ta kaddamar da dan takararta
2015-01-09 10:23:02 cri

A jiya ne jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta kaddamar da dan takararta na zaben shugaban kasa a birnin Legas, cibiyar kasuwannin kasar, gabanin zaben shugaban kasar da za a yi a watan Fabrairun wannan shekara.

Dubban magoyon bayan jam'iyyar daga jihohi 36 da kuma Abujan ne suka yi dandanzo a dandalin Tafawa Balewa da ke birnin na Legas.

Daga cikin wadanda suka halarci kaddamarwar sun hada da mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, shugaban majalisar dattawan Najeriya David Mark, shugaban Jam'iyyar PDP na kasa Adamu Mu'azu, gwamnonin jam'iyyar PDP da shugaban kungiyar gwamnonin Godwil Akpabio ya jagoranta.

Jam'iyyar ta PDP dai ta tsayar da shugaba Jonathan ne a matsayin wanda zai yi mata takara a zaben shugaban kasar, inda zai fafata da janar Muhammadu Buhari mai ritaya na babbar jam'iyyar adawar kasar wato APC.

Tun a makon da ya gabata ne jam'iyyar ta APC ta kaddamar da nata dan takarar a garin Fatakwal na jihar Rivers mai arzikin mai. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China