in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane miliyan 68.83 suka yi rajista domin kada kuri'a a zaben Nigeria
2015-01-14 10:21:39 cri

Hukumar zabe ta Nigeria ta kammala kididdigar adadin jama'ar da suka yi rajista domin taka rawa a zaben kasar da aka shirya gudanarwa a watan Fabarairu mai zuwa.

Shugaban hukumar zaben ta Nigeria Attahiru Jega, wanda ya yi jawabi a yayin wani taron manema labarai ya ce, kawo ya zuwa yanzu 'yan Nigeria fiye da miliyan 68 ne suka yi rajista domin taka rawa a babban zaben kasar da za'a yi a bana.

Jega ya ce, hukumar zaben ta gano cewar, adadin 'yan Nigeria 68,833,476 ne suka yi rajisata bayan an debe gurbatattun rajista da wasu suka yi har fiye da miliyan 4 daga cikin adadin masu rajista na kasar miliyan 73.5.

Shugaban hukumar zaben ya kuma gabatar da rajistar masu kada kuri'a ga jam'iyyun siyasa na kasar.

Jega ya kara da cewar, nan da 'yan kwanaki za'a buga wannan adadi a kan shafin sadarwa na Internet na hukumar zaben ta Nigeria.

Shugaban hukumar zaben ya ce, kawo ya zuwa yanzu jam'iyyun siyasa na kasar sun zabi 'yan takarar 14 wadanda za su tsaya takara domin kokowar matsayin shugaban kasa a zaben da za'a yi a ranar 14 ga watan Fabarairu. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China