Dan takarar jam'iyyar adawa ta APC a Nigeriya Muhammadu Buhari ya yi alkawarin inganta sauran hanyoyin samar da arziki ga kasar da ba na man fetur ba, idan har ya samu nasarar babban zabe.
Dan takarar na APC ya yi wannan alkawarin ne a gangamin neman zaben da aka yi a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun dake kudu masu yammacin kasar.
A nashi ra'ayin, dogaro gaba daya a kan albarkatun man da kasar ke da shi da kuma rashin kula da albarkatun da gwamnati ke yi sun sa tattalin arzikin kasar fadawa cikin halin wuya da yanzu haka ake fuskanta. Don haka ya yi alkawarin shawo kan wannan al'amari idan har aka zabe shi shugabancin kasar.
Yana mai lura da cewa, matsayin ilimi a kasar ya fadi warwas, a nan kuma ya ba da tabbacin cewa, gwamnatin APC za ta samar da yanayi mai kyau na samun ilimi saboda takardun shaidar ilimi na jami'o'in kasar ya sake dawo da martabarsa a idon kasashen duniya. (Fatimah)