Shugaban kasar Nigeria Goodluck Jonathan ya dauki alkawari na rage kalubalen ta'addanci a kasar idan dai har an zabe shi a babban zaben da za'a yi a kasar a watan Fabarairu mai zuwa.
Shugaban na Nijeriya wanda ya yi magana a yayin taron kamfe na jam'iyyar PDP, wanda aka yi a jihar Osun a kudu maso yammacin kasar, ya ce, matsalar da kasar ke fuskanta a bangaren tsaro ba wani abu ba ne da zai ci gaba da kasancewa har abada, saboda haka ya ce, idan an zabe shi, matsalar ta'addanci za ta ragu ainun.
Jonathan ya ce, a ko wace shekara matasa miliyan 1 da dubu dari takwas ke shiga cikin sahun masu neman aiki a Nijeriya, kuma saboda haka idan aka kara zaben shi, gwamnatinsa za ta ci gaba da magance matsalar rashin aikin yi ta hanyar samar da guraban ayyukan yi miliyan 2 a ko wace shekara.
Jonathan ya ce, kokarin da gwamnatinsa ta yi a fannin jirgin kasa da ayyukan noma, da wutar lantarki sun isa dalili na kara zaben shi a zaben da za'a yi. (Suwaiba)