An sanya hannu a kan wata yarjejeniyar amincewa tsakanin kasar Sin da kasar Madagascar domin karfafa hulda a fannin binciken yanayin kasa.
A jiya Laraba ne jami'ar Antananarivo ta Madagascar, da jami'ar nazarin ilmin yanayin kasa ta kasar Sin dake birnin Beijing, da kuma hukumar binciken yanayin kasa ta kasar Sin, suka sanya hannu a kan yarjejeniyar gudanar da aikin gamayya da juna.
Mr. Xi Xuewen, mataimakin shugaban jami'ar nazarin ilmin yanayin kasa ta kasar Sin, wanda ya jagoranci wata tawagar wakilai 4 ta kasar Sin domin gudanar da aikin kwanaki 3 a Madagascar ya bayyana a cikin jawabinsa cewar, yarjejeniyar da aka rattaba hannu a kai, za ta taimakawa Madagascar bunkasa tattalin arzikinta, tare da kara dankon zumunta tsakanin kasashen 2.
Shugaban jami'ar Antananarivo Panja Ramanoelina, ya ce, yarjejeniyar za ta baiwa malaman makaranta da dalibai na Madagascar wata dama ta kirkiro da taswirar albarkatun kasar, tare kuma da kara karfafa musayar dalibai da sheihun malamai tsakanin Sin da Madagascar. (Suwaiba)