Zaman taro karo na 34 na shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashen mambobi na kungiyar SADC, da ya gudana a birnin Victoria Falls na kasar Zimbabwe, daga ranakun 17 da 18 ga watan Agusta, ya bukaci da a aiwatar jadawalin aikin da aka cimma domin fitar da kasar Madagascar daga rikicin siyasa, a cewar wata sanarwa ta kungiyar SADC a ranar Laraba.
Game da batun kasar Madagascar, dandalin ya jaddada niyyarsa na tallafawa kasar a cikin tsarin shawarwari da sasantawa da kuma batun sake gina kasar, in ji wannan sanarwar. (Maman Ada)